Kamfanin Facebook ya sanar da cewa yana gwajin hanyar da zai rika isarwa da mutane labaran dake fitowa a shafinsa, wajen raba labaran da suka shafi tallar kamfanoni da kuma bayanan da mutane ke kafewa a shafinsu. Wanda ake ganin yin hakan zai sa ‘yan kasuwa su kara azamar yin talla a shafin Facebook.
Hanyar yada labarai a Facebook guda daya ce tal, wadda ke zama wata muhimmiyar abu a babban shafin dandalin sada zumunta a fadin duniya. Abubuwan da ke fitowa a shafin sun hada da yadda ake kafe dubban hotuna daga ‘yan uwa da abokan arziki, sai kuma talla da wasu kamfanoni ke yi, har ma da bayanan da wasu jarumai ke tafewa da dai sauransu.
Facebook na yin wannan gwaji ne a wasu kananan kasashe guda shida, wanda yanzu haka a kasasehen ake da hanyoyin samun labarai har guda biyu, daya na mayar da hankali ne akan abubuwan da mutane suka kafe, ta biyun kuma kacokan ta dogara ne akan shafukan da mutum yake so.
Wannan sauyi da Facebook zai kawo ka iya tilastawa wasu dake da shafi da suka hada da kamfanonin yada labarai da mawaka zuwa kungiyoyin wasanni, su biya kudin talla idan har suna son abubuwan da suke kafewa ya kai ga jama’a.
Your browser doesn’t support HTML5