Kamfanin Equifax Zai Biya Tarar Sama Da Dala Miliyan $700

Equifax

Kamfanin Equifax zai biya kusan dala miliyan $700M don biyan tarar da hukumar harkokin cinikayyar Amurka da wasu ma’aikatu, kan sakacin da yayi aka yi masa kutse a shekarar 2017. Inda aka samu wasu muhimman bayanai na mutane da aka sata, ciki har da lambobin bayanan sirri na kusan mutane miliyan 150.

Wadannan kudaden tara da za su biya ofishin da yake sa ido akan cibiyoyin kudi a Amurka, idan har alkalin tarayya na gundumar Arewacin Georgia ya amince, zai sa a yafewa mutane masu amfani da kudaden bashin da suka kai kusan dala miliyan $425M. Sannan za’a ci su tara ta dala miliyan dari $100 na kudaden da za’a biya jama’a.

Ofishin ya shirya bincike tare da hukumar harkokin cinikayyar Amurka da kuma Atoni Janar daga jihohin Amurka gaba daya.

Sai dai sanarwar ta jiya litinin ta tabbatar da rahoton mujallar Wall Street, cewa hukumar da ke karbar bayanan ba da rance ta cimma matsaya tare da gwamnatin Amurka.