Kamfanin Boeing Ya Dakatar Da Sayar Da Samfurin Jirgin MAX 737

Biyo bayan hadarin da kamfani jirgin sama na Ethiopia ya yi, kamfani Boeing ya dakatar da saida samfurin jirgin da kamfanin yake kerawa.

Kamfanin Boeing ya sanar jiya Alhamis cewa, ya dakatar da sayar da samfurin jirgin MAX 737 ga kamfanonin jiragen sama, bayan da kusan duka kasashe suka dakatar da amfani da jirgin biyo bayan wani mummunan hadari da jirgin Ethiopia ya yi ranar Lahadi wanda ya hallaka mutane da dama.

Mai magana da yawun kamfanin Boeing, ya ce za su ci gaba da kera samfurin jirgin MAX 737 tare da yin la’akkari da wasu matsaoli da ka iya tasowa, wadanda za su iya shafar hada wannan jirgi.

Hakan na nufin yayin da kamfanin Boeing zai ci gaba da kera samfurin wannan jirgi, zai dakatar da rarraba shi har sai an saka sabuwar manhaja, an gudanar da gwaje-gwaje, kuma a samar da bayanai kan musabbabin hadarin jirgin Ethiopia.

Hadarin da jirgin saman Ethiopia 737 MAX 8 ya yi ranar Lahadin jim kadan bayan ya tashi daga Addis Ababa ya kashe mutane 157.

Baya ga wannan, wani jirgin MAX 8 ya fadi a Tekun Java mintina kadan bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Indonesia a watan Oktoba inda ya halaka dukkan fasinjojin da suke cikin jirgin su 189.