Kamfanin BMW Zai Fara Kera Motoci Masu Sarrafa Kansu

Tambarin Kamfanin BMW

Kamfanin BMW da Intel da Mobileye sun hada kansu domin kirkirar mota mai sarrafa kanta ta hanyar amfani da na’urar daukar hoto mai gani har hanji, wadda kuma ake ganin nan da shekaru goma masu zuwa zasu fitar da ita.

A wani taron manema labarai da kamfanonin uku suka gabatar a kasar Jamus, sun fayyace shirin su na kirkirar wannan fasaha ta mota mai sarrafa kanta zuwa shekara ta 2021.

Duk da cewar irin wadannan motoci suna samun hatsari a kwanannan, wanda cikin makon da ya gabata ma an sami wata motar kamfanin Tesla dake tuka kanta tayi hatsari har direban motar ya rasa ransa. Manya manyan kamfanoni na gasa tsakanin junansu wajen ganin an samar da sabuwar fasahar da zata rage yawan hatsarin da ake samu.

Masana dai na cewa akwai bukatar samar da ingantacciyar fasaha kafin ire iren motocin su fara aikin daukar mutane ba tare da fargaba ba.

Shidai kamfanin Mobileye yayi fice wajen kera na’urorin mai gani har hanji, shi kuma kamfanin Intel an sanshi a duniya wajen kera na’urar processor da ake amfani da su a kwamfutoci. Hakan yasa ake ganin tabbas dole ayi tsammanin kamfanonin zasu fitar da motar azo a gani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin BMW Zai Fara Kera Motoci Masu Sarrafa Kansu - 1'09"