Kamfanin Blackberry Ya Daina Kera Wayoyin Hannu

Shugaban Blackberry John Chen

Shugaban Blackberry John Chen

Bayan kwashe shekaru 15 cikin harkar kirkirar wayoyin hannu, kamfanin Blackberry ya fitar da sanarwar cewa ya daina kirkirar wayoyin zamani.

Kamfanin wanda yayi fice kan yadda ya ke kirkirar wayoyinsa wanda ke jan hankalin kwararru kan kowanne fanni, ya dade yana fama wajen zama kafada da kafada da sauran takwarorinsa kamar su Apple da Samsung a lokacin da wayoyi suka canza a duniya.

A sakamakon haka ne, kamfanin ya yanke shawarar cewa zai mayar da hankali wajen kirkirar manhajar wayoyin zamani, maimakon wayoyin kansu. Sai dai ya rinka kerawa wasu kamfanoni.

Kamar yadda shugaban kamfanin John Chen, ke cewa “kamafanin na shirin kawo karshen kirkirar wayoyi, sai dai yayiwa wasu kamfanoni aiki. Ya ci gaba da cewa zamu mayar da hankali wajen kirkirar manhajojin waya.”

Wannan labari na zuwa ne lokacin da kamfanin Blackberry ya fitar da rahotan cewa yayi asarar kudi Dalar Amurka Miliyan 372 cikin watanni ukun da suka gabata, idan aka kwatanta da ribar da kamfanin ya samu ta Dala Miliyan 51 kamar ya wannan lokaci a shekarar da ta gabata. Kasuwar Blackberry dai ta fadi warwas cikin wannan shekara.