Kamfanin Apple Zai Rufe Rassansa

Wani mutum yana tafiya a gefen ginin kamfanin Apple da aka rufe a birnin Beijing, ranar 4 ga watan Fabrariru 2020. Mark

Kamfanin Apple ya ce zai rufe daukacin shagunansa a duk fadin duniya har na tsawon mako biyu, a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus, a cewar shugaban kamfanin Tim Cook.

A wata sanarwa da ya fitar a karshen makon da ya gabata, Cook ya nuna cewa, “hanya mafi inganci da za a iya takaita yada cutar ita ce a kauce wa haduwar jama’a.”

Sai dai kamfanin ya ce, zai ci gaba da yin hada-hada ta yanar gizo da kuma manhanjarsa.

Baya ga daukan wannan mataki, kamfanin na Apple ya ce zai ware dala miliyan 15 domin taimakawa a yakin da duniya ke yi da cutar.

Shi dai kamfanin na Apple na da rassa kusan 500 a duk fadin duniya, inda kusan rabin wannan adadi a nan Amurka suke.

Tun a lokacin da cutar ta barke a China, kamfanin na Apple ya rufe rassansa da ke Chinan - kasar da cutar ta coronavirus ta fara bulla.