Taron da suka yi a gabar kogin Neja dake da iyaka da jamhuriyar Benin ya tabo batutuwa da dama da suka shafi hadin kan kasa da kuma irin nasarar da gwamnatin Najeriya ta samu a yakin da ta keyi da 'yan kungiyar Boko Haram.
Farfasa Muhammad Yakubu Aula shugaban kungiyar ta Kambari a Najeriya yace suna godiya ga shugaban kasa Muhammad Buhari domin hobasar da yayi na koran 'yan Boko Haram.
Tsohon gwamnan jihar Kano wanda jigo ne a kungiyar kabilar Kambari Kanar Aminu Isa Kontagora yace duk da nasara da aka samu akan 'yan Boko Haram akwai abun da ya rage. Yace yanzu lokaci ne da za'a nemi shugabannnsu a zauna dasu a ji abubuwan dake damunsu domin su san cewa Najeriya ta fi karfin kowane mahaluki.
A wani jefe guda kuma mahalarta taron sun yi korafi kan halin rashin ababen more rayuwa da suke fama dashi.
Shugaban matasan kabilar ta Kambari Bala Bitajir yace wani da ya kai rafin dake kusa dasu ba zai wuce nan ba balantana ya san akwai wata karamanr hukuma a yankin. Ya kira a zo a duba yanayin da suke ciki domin a taimaka masu.
Shugaban karamar hukumar Agwaran Onarebul Jafaru Muhammad Ali yace rashin gada a kogin Zamare na ci masu tuwo a kwarya. Yace da zara an gina gadar ana iya tafiya Ibadan ko jamhuriyar Benin. Ya kira gwamnati tayi masu alfarma da gina masu gadar tare da hanya.
Akwai kambarawa kimanin miliyan shida a Najeriya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5