Ya Kamata A Fifita Rubuce-Rubuce A Fannin Tarihi Don Raya Najeriya Da Nahiyar Afurka - Khalid Zaria

Marigayi Sanata Abubakar Olusola Saraki.

Fitaccen marubuci kuma mai karantarwa a Najeriya, Mal. Khalid Abdullahi Zaria ya ce kusan kullum ana yin musu a kan abubuwan da suka shafi tarihi a kasar, kama daga kaka da kakanni, addini, zuwan bayajidda da dai sauransu.

Lamarin da a cewarsa rashin litattafan tarihi da rubuce-rubuce da suka haura shekara 100 da rubutawa ke kara mayar da hannun agogo baya wajen ilmantar da matasa a kasar.

Marabuci Khalid ya yi misali da litafinsa na 155 inda ya yi rubutu a kan marigayi tsohon sanata daga jihar Kwara Dakta Olusola Abubakar Saraki sakamakon yadda ya kasance da nuna kauna da ‘yan uwantaka tsakanin iyakar arewa da kudu duk da cewa ya yi kusan duk rayuwarsa ne a kudu bayan dawowa daga kasar Burtaniya a matsayinsa na likita.

Khalid, wanda ke rubuta tarihin mutane wadanda su ka damu da ci gaban al’ummarsu da yadda zasu ci moriyan ababen da suka yi har duniya ta nade, ya jaddada mahimmancin rubuta tarihin Najeriya, musamman kasar hausa, bisa la’akari da yadda babu litattafai kan tarihin yankin.

Labarin yadda marigayi Dakta Olusola Abubakar Saraki ya fifita dan arewa a lokacin da aka bukaci ya bada shawara kan mataimakin shugaban kasa da ya kamata ya gaji marigayi Umaru Musa Yar’adua tsakanin dan cikinsa da Namadi Sambo kuma ya zabi dan arewa, abu ne da ya kamata a rubuta a yadda domin sanar da cewa akwai dattawan Najeriya wadanda ke raye ko sun riga mu gidan gaskiya da suka yi kishin al’umma a rubuce don tarihi in ji Khalid Abdullahi Zaria.

Ku latsa wannan sauti domin jin cikakken bayani a kan mahimmanci karfafa rubuce-rubuce kan tarihin Nahiyar Afurka musamman ma Najeriya da kuma harshen Hausa.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamata A Fifita Rubuce-Rubuce A Fannin Tarihi Don Raya Najeriya Da Nahiyar Afurka - Khalid Zaria