Gwamnatin Kamaru ta dau aniyyar sake bude babban kamfanin sarrafa alkama a jihar Adamaoua da fatan zai taimaka wajen sawaka ma al’umar kasar domin samar da burodi, daya cikin nau’ukan kayan abinci da aka fi amfani da su.
An ƙirƙiro wannan kamfani a 1975 a Wassande a jihar Adamaoua sai dai abin takaici SODIBLE ya rufe kofofinsa a ƙarshen 1989.
Sai dai kuma a cikin ‘yan shekarun nan, gwamnatin Kamaru ta yi niyyar sake bude wannan kamfani na noman alkama, amma kuma tana fuskantar wasu matsaloli, musamman tsadar takin zamani, sakamakon tashin hankali da ke gudana tsakanin Rasha da Ukraine.
Abdullahi Mansoor, manomi ne kuma mazaunin Yankin Adamawa, ya yi farin ciki da wannan labari, ko da yake yana taka-tsantsan da irin wannan alkawari na gwamnati.
Wasu manoma sun shawarci gwamnati da amfani da takin gargajiya maimakon takin zamani mai dauke da sinadarai na magunguna domin a cewarsu, hakan zai iya rage kashe kuɗi mai yawa.
Manoman sun kara da cewa don gudun tsadar takin sinadarai sun koma amfani da kashin kaji.
Idan alkama ita ce hatsin da ake buƙata sosai a Kamaru don samar da burodin da ake amfani da su sosai, Ministan Noma da Raya Karkara Gabriel Mbairobe yana ƙarfafa ’yan uwansa da su koma samfuran rogo ko masara, kafin a bai wa SODEBLE damar cinma wannan buri.
Saurari cikakken rahoton Mohamed Bachir Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5