Kamaru Ta Zama Kasa Ta Farko Da Ta Shiga Zagayen 'Knockouts' A AFCON

Dan wasan Kamaru Vincent Aboubakar a lokacin da yake zura kwallo a ragar Ethiopia.

Kamaru dai ta ci wasanninta biyu, inda ta doke Burkina Faso a wasanta na farko a rukuninsu na A.

Kyaftin din Kamaru Vincent Aboubakar da Karl Toko Ekambi, sun zura kwallaye biyu-biyu a ragar Ethiopia a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

An tashi a wasan ne da ci 4-1 inda Kamarun ta lallasa kasar ta Habasha wacce ta fara zura kwallon farko a ragar Kamaru mai karbar bakuncin gasar.

Wannan nasara ta ba Kamaru damar shiga zagayen iyawarka-ta-fitar-da-kai inda za a fara sallamar kasashe zuwa gida a zangon na ‘yan 16.

Kamaru dai ta ci wasanninta biyu, inda da ta doke Burkina Faso a wasanta na farko a rukuninsu na A.

A halin da ake ciki Burkina Faso ta doke Cape Verde da 1-0 bayan kaye da ta sha a hannun masu masaukin bakin.

A ranar Juma’ar nan Gabon za ta fafata da Ghana, inda dan wasanta Pierre-Emerick Aubameyang zai dawo daga kebe kansa da ya yi.

Gwaji ya nuna Aubameyang na dauke da kwayar cutar COVID-19 yayin da suka sauka a kasar ta Kamaru a makon da ya gabata, lamarin da ya tilasta masa ya kebe kansa kamar yadda AP ya ruwaito.