A wani jawabi da ba a saba gani ba, da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi, ya ce, ya umarci Firayim Ministan kasar da ya shiga tattaunawar hadin kai a kan matsalolin da ke damun kasar, ciki har da tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 2,000 a rikicin Yankunan masu amfani da harshen ingilishi. Haka kuma Biya ya kara da cewa yana kira ga kasashen waje da su taimaka masa don dakatar da ‘yan kasar Kamaru dake kasashen waje daga daukar nauyin tashin hankalin a gida.
Biya ya yi kira ga dukkan mayakan da ke Yankin masu magana da harshen Ingilishi dasu mika wuya, kuma za’a yafe musu, idan ba hakaba to zasu fuskanci sojansa.
‘Yan Kamarun sun yi tsammanin cewa, Biya zai yiwa shugaban 'yan aware Julius Ayuk Tabe afuwa, , wanda shi da wasu mutane tara magoya bayansa, aka yanke musu hukucin daurin rai da rai a gidan yari, makwanni biyu da suka gabata, wadanda suka haddasa hare-hare kan gine-ginen gwamnati a yankuna da ke magana da harshen Ingilishi da kuma yaudarar jama'a.
Mayakan 'yan awaren sun sha alwashin mayar da yankunansu su zama saniyar ware tare da dakatar da makarantu daga budewa a watan Satumbar da ya gabata har sai an saki shugabanninsu ba tare da wani sharadi ba.