Rundunar Sojin Kamaru Ta Ce An Kashe Sojanta A Wani Harin Kwanton Bauna Da ‘Yan Jihadi Suka Kai

Yan Bindiga

Yan Bindiga

Majiyoyin soji da na cikin gida sun sanar a jiya Juma’a cewa wani harin kwantan bauna da mayakan jihadi suka kai a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru ya hallaka wani soja.

An kai harin ne a ranar Alhamis a garin Ldaoussaf da ke yankin da ke fama da rikicin masu tada kayar baya na jihadi, kamar yadda majiyoyin biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, da suka nemi a sakaya sunayensu.

“An kai wa wani jami’in sintiri kwanton bauna,” in ji wani babban jami’in soji, ya kuma kara da cewa an kashe soja daya, wani kuma ya jikkata. "Maharan sun gudu da makamai."

Wani wakilin karamar hukumar wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da adadin mutanen.

A shekarun baya-bayan nan dai kungiyar Boko Haram ta Najeriya da kuma reshenta na 'yan ta'addar yankin yammacin Afirka (ISWAP) na ci gaba da kai munanan hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a arewacin Kamaru, da ma wasu sassan Najeriya da Nijar da kuma Chadi.

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009 kafin ta yadu zuwa wurare da dama.

Sama da mutane 36,000 ne aka kashe tun daga lokacin, musamman a Najeriya, kuma mutane miliyan 3 ne suka tsere daga gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.