Kamaru Na Raba Dabbobi Don Yakar Boko Haram

Dabbobin da ake rabawa mutane a kasar Kamaru.

Kasar Kamaru ta shiga rarraba dubban awaki da tumaki ma mutanen da ke kauyukan kan iyakar arewacin kasar da ke tsakaninta da Najeriya, da zummar kawo karshen shiga kungiyar Boko Haram da matasan kauyukan marasa ayyukan yi ke yi.

Ana kyautata zaton kiwon dabbobin zai samar wa dubban iyalan da ka iya sauraran Boko Haram abin zaman gari, ta yadda ba za su rika kwadayin shiga tsattsaurar kungiyar ba, da kan rinjaye su da alkawarin samar da ayyukan yi.

Gwamnatin kasar Kamaru, wannan satin, ta fara bullowa da wani irin makamin yakar Boko Haram, wanda ba a saba gani ba.

Hukumomi na rarraba dubban tumaki da awaki ma matasan da ke kauyukan kan iyakar kasar da Najeriya.

Manufar wannan shirin ita ce wanzar da dabbobin kiwo a matsayin abin samar da kudin shiga, saboda a taka birki ma mayaka masu tsattsauran ra’ayin addini, wadanda kan yi amfani da dabaru wajen samo mabiya.

A kauyen Salak, an bai wa malama Nafisatu Umar ‘yar shekaru 17 tumaki hudu.

Nafisatu ta ce ta zaku ta ga tumakinta sun hayayyafa saboda ta sayar ta biya kudin makaranta. Ita ce ke daukar nauyin kanta, a cewarta, bayan mutuwar mahaifinta da mahaifiyarta.

Mayakan Boko Haram sun hallaka iyayen Nafisatu da wasu mutane 21, lokacin da su ka kai hari a kauyensu a 2017, wanda don haka ta gudu.

Bayan mako guda kawai, sai ‘yar’uwar Nafisatu ta tarwatsa kanta a wani harin kunar bakin wake da ta kai wani masallaci da ke kauyen Kolofata. Kungiyar Boko Haram ce ta yaudare ta, cewa za ta samar ma ta da aikin yi a matsayin mai goge-goge a gidaje, amma daga bisani ta tilasta ma ta kai harin kunar bakin wake.

Gwamnatin Kamaru dai ta yi alkawarin rabar da awaki da tumaki 60,000 zuwa karshen shekara. Ministan Albarkatun Dabbobi na kasar, Dr. Taiga, ya ce za a raba dabbobin kiwon ne ma wadanda yaki da Boko Haram ya rutsa da su.

Ya ce manufar shirin shi ne a agaza ma iyalan da su ke fuskantar hadari ta wajen samar da dabbobin da ke iya hayayyafa kuma za su iya samar masu da kudi. Dabbobin za su samar masu da abin rufin asiri, a cewar Taiga, ta yadda za su iya kula da iyalansu, su kuma bayar da gudunmowarsu ta wajen kauce ma yaudarar da ka iya illa ga zaman lafiya ko haddasa rudami.

Hukumar Raya Tafkin Chadi, mai mambobin kasashe takwas a yankin, ciki har da Kamarun, ta ce wasu wuraren da Boko Haram ta kai wa hare-hare su na da rashin ayyukan yi da kashi 90%.

Mijinyawa Bakary, gwamnan yankin Arewa Mai Nisan a kasar Kamaru, ya lura cewa babu wani mummunan hari da Boko haram ta kai bara, to amma ya ce mayakan na Boko Haram na cigaba da neman mabiya, don haka sojoji sun daura damara.

Ya ce yakamata mutane su kula sosai saboda ‘yan Boko Haram na yaudarar matasa marasa ayyukan yi ta wajen yin masu alkawarin inganta rayuwarsu. Ya kamata a farfado da ayyukan ‘yan banga a kauyuka su rika hada kai da sojoji, da jami’ai, da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, a cewar Bakary. Ya ce su na iya musayar bayanai game da duk wani take-taken da ake ganin ka iya shafar zaman lafiyan da ya fara dawowa a kauyuka da garuruwa.

Domin karin bayani saurari rahotan cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamaru Na Raba Dabbobi Don Yakar Boko Haram - 3'18"