Ministan kiwon lafiyar kasar ta Kamaru ya rabtaba hannu a kan yarjejeniyar da suka kulla a madadin gwamnatin kasarsa.
An shirya taron ne tsakanin kasar da kungiyoyin uku da suka fito daga Faransa da zummar yakar cutar farfadiya a kasashen dake yankin Afirka ta tsakiya.
Kasar Kamaru ce ta karbi bakuncin taron da aka yi a Yaounde dake zama babban birnin kasar.
Ministan kiwon lafiya na Kamaru yace ciwon farfadiya nada la'ani ainun wanda ya fi yawa a jihohin Adamawa da da na arewacin kasar su ne suke fama da cutar..Alkalumma sun nuna cewa wajen 20 cikin dari na jama'ar jihohin ke fama da cutar wadda ta zama masu annoba. A duk fadin Afirka kuma kasar Kamaru ce take kan gaba a cutar.
A taron ministan cikin gida na kasar ta Kamaru ya gayyaci malaman addinin musulunci da na kirista su yi wa kasar addu'a da kuma maniyattan kasar da suka kwanta dama a turmutsitsin da ya auku a Saudiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5