KAMARU: An Gano Sabbin Mutane 3,157 Da Suka Kamu Da Cutar Kanjamau A Shekarar 2021

Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS)

Hukumar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS), ta ce mutane dubu 3,157 ne suka kamu da cutar kanjamau a kasar Kamaru a shekarar da ta gabata. Wannan ya nuna cewa an samu ci gaba wajen yaki da wannan cutar. 

Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS), ta bayyana sabon rahoton ne, yayinda kasashen duniya ke kara kaimi a yaki da cutar ta wajen fadakar da al'umma a ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya.

A cewar kungiyar, dangane da "kididdigar nauyin cutar kanjamau" da aka samar a wannan shekara, Kamaru ta sami sabbin mutane 3,157 da suka kamu da cutar a cikin 2021.

Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS)

UNAIDS ta kara da cewa, wannan yana daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da aka samu a kasashe 13 na Afirka da ke cin gajiyar kudade daga asusun duniya don yaki da cutar AIDS, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.

A fadin likitoti da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, wannan labarin ya nuna cewar an samu ci gaba a yaki da cutar kanjamau a Kamaru

A bayanin sa, kwararren likita Dr Adamu Kasim yace wannan ci gaba da aka samu na da asali kan iri' aikin da 'yan jaridu suka yi wajen fadakarwa.

Dr Adamu Kassim ya ƙara da cewa za' a iya samun nasara fiye da haka idan aka kara kaimi.

Adadin mutanen da ke bukatar maganin cutar kanjamau a zahiri da ke jinya ya karu sosai a cikin shekaru goma da suka gabata, daga 23% a cikin 2010 zuwa 75% a 2021.

Saurari rahoton Mohamed Bachir Ladan cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KAMARU: An Gano Sabbin Mutane Dubu 3157 Da Suka Kamu Da Cutar Ƙanjamau A Shekarar 2021