Kama Akanta-Masu Sharhi Na Cigaba Da Karfafawa EFCC Gwiwa Kan Yaki Da Barayin Biro

  • Saleh Shehu Ashaka

EFCC

Masu sharhin na cewa ya na da kyau hukumar EFCC ta rika nuna ba sani ba sabo ga masu zarmiya don ta hakan ne kadai za a ceto Najeriya daga koma baya.

Biyo bayan kama babban akantan Najeriya Ahmed Idris a makon jiya da tuhumar almundanar Naira biliyan 80, masu sharhi na kara karfafawa hukumar EFCC gwiwa ta kara dagewa ga yaki da barayin biro.

Masu sharhin na cewa ya na da kyau hukumar ta rika nuna ba sani ba sabo ga masu zarmiya don ta hakan ne kadai za a ceto Najeriya daga koma baya.

Shugaban kungiyar tabbatar da adalci ta CISLAC Auwal Musa Rafsanjani ya ce tamkar gwamnatin Buhari da ta fi kururuwa da yaki da barayin, ta zama tamkar mai dokar barci ne.

Ku Duba Wannan Ma Yadda EFCC Ta Gurfanar Da Rochas Jim Kadan Bayan Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023 

Shi kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum Bashir Baba ya duba ahuwa da gwamnati ta yi wa wadanda a ka yankewa hukuncin zarmiya da cewa ko an kama irin wadannan jami'an wataran za a iya wanke su.

Hukumar EFCC na cewa ta kan yi aiki ne ba don bita-da-kulli ba, amma koyaushe mukarraban wanda ya fada komar hukumar kan kawo dalilan wani rashin jituwa ne ya sa a ka sanya ma sa kahon zuka.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kama Akanta-Masu Sharhi Na Cigaba Da Karfafawa EFCC Gwiwa Kan Yaki Da Barayin Biro