Farmakin mayakan Boko Haram da na ‘yan ta’adda masu satar mutane domin karbar kudin fansa shi ne babban kalubalen da ya dabaibaye yankin arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin Najeriya a yanzu.
Baya ga hana galibin manoma aiki da tsageran suka yi a daminar bana, babbar matsalar da ke wakana a yanzu ita ce farmakin da suke kai wa gonakin manoma kalilan da suka samu zarafin yin noma a bana.
Hari na baya-bayan nan shine wanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai inda suka kashe manoma fiye da 40 a jihar Borno a karshen makon da ya shude.
Jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto na cikin wadanda ke sahun gaba wajen fuskantar wannan kalubale.
Malam Mustafa Muhammad Dandume, Malamin addini kuma manomi a jihar Katsina, ya bayyana cewa shi kansa ya kashe kudi sosai don aikin gona amma mahara sun sa noman ya gagara a bana. Ya kuma ce akwai maciya amana da marasa tsoron Allah da ke yin zagon kasa a Najeriya.
Sai dai, dattawa irin su Abdulkarim Dayyabu na cewa gaskiya gaskiya ce sai dai a ki yin amfani da ita, kundin tsarin mulki a ko ina a duniya ana yin shi ne don wasu muhimman abubuwa da suka hada da kare rayukan al’umma, dukiyarsu, mutuncinsu, da addinisu, duk abinda ya gaza haka to babu gwamnati, a cewarsa.
To amma wasu na ganin gazawar gwamnati wajen aiki da shawarwarin masana da kwararru da sauran ‘yan kishin kasa, ya taka rawa wajen tabarbarewar al’amura a yankin arewacin Najeriya.
Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, na tsangayar nazarin Ilimin gudanar da mulki a Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce an dade ana yin kiraye-kirayen kafa ‘yan sandan jihohi amma gwamnati ta turje kuma ba tare da ta dauki matakin magance matsalar ba.
Ga cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5