Fatahiyya Bature Adam, wata matashiya ce da take neman gurbin karatu a makarantar gaba da sakandare ta ce, bisa al’adar neman gurbin karatu a Najeriya, bayan ta kammala makarantar sakandare, ta nemi gurbin karatu a fannin Political Science wato ilimin kimiyyar siyasa amma hakkarta ba ta cimma ruwa ba.
Fatahiyya ta ce, ta nemi gurbin karatu a makarantar a Aminu Kano College of Legal studies inda aka ba ta fannin harshen Ingilishi hade da fannin ilimin yanayin kasa, wato Geography bayan da ta nemi Political Science ba ta samu ba.
Ta kara da cewa “Babban kalubalen da na fara cin karo da shi, shi ne , tashin farko mu kimanin dalibai 400 da wani abu ne a aji, a yayin darasi kuwa idan malami na koyarwa duk wanda ya ji, ya ji wanda bai sa hankali ba za’a bar shi a baya.”
Sakamakon cunkoson da ake da shi a ajujuwa, Fatahiyya ta ce, yanayin koyarwa ba yadda ta yi tsamani ba ne, domin ba kasafai ake jin abin da malami ya ke koyarwa ba duk da cewar wani lokacin akan yi amfani da amsa amo wato loud speaker, domin daliban da suke baya su ji abin da malami ya ke koyarwa.
Bayan kammala karatun NCE, Fatahiyya ta ce sai ta nemi aiki a wata makarantar firaimare inda ta fara koyarwa ga dalibai ‘yan aji hudu
A cewar Fatahiyya, koyarwa ya na da na sa kalubalen, a mafi yawan lokutan idan tana kokarin daidaita ajin na ta sai wani bangare na dalibai ya balle da surutu ko rashin ji.
Your browser doesn’t support HTML5