Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tattalin Arziki – Masana

Dr. Doyin Salami (Facebook/Doyin Salami)

Wasu ‘yan kasar na ganin wannan nadin na zuwa ne a kurarren lokaci  kamar yadda Usman Ma’azu ke cewa. 

Kasa da watanni 17 mulkin shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya ya zo karshe, masana sun bayyana cewa akwai jan aiki a gaban sabon nadin da ya yi wa Dakta Doyin Salami a matsayin mai ba shi shawara kan sha’anin tattalin arzikin kasa.

Duk da kwarewar da Dakta Doyin Salami ke da ita a matsayin Shugaban kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki a Najeriya masana daga wannan bangaren sun bayyana cewa akwai tarin kalubale da ke gaban wannan sabon nadi da aka yi masa duba da yadda a lokuta da dama ake samun rashin aiwatar da wasu tsare- tsare sakamakon karo da suke da juna.

“Akwai matsaloli na wani lokaci a yi wani tsari wani kuma ya zo ya rushe wani, wanda yake kalubale ne ga shi wannan Farfesa Doyin Salami, ya kamata a ce ya tsaya ya ga duk yadda za’a yi a Najeriya farashin abinci da kayan masarufi ya sauko saboda talakawan kasa su samu saukin rayuwa.” A cewar Dakta Isa Abdullahi na sashen nazarin tattalin arzikin kasa da ke jami’ar kashere na jihar Gombe.

Sai dai kuma wasu ‘yan kasar na ganin wannan nadin na zuwa ne a kurarren lokaci kamar yadda Usman Ma’azu ke cewa.

“Za’a iya kiranshi ihu bayan hari, kasancewar kasa da watanni goma sha bakwai kacal ya rage ma shugaba Muhammadu Buhari da ya yi hakan batun yau ba abun zai haifar da da mai ido ba, amma ganin kurewar lokacin da kuma yadda da shi kan shi tattalin arzikin ya jigata, abu ne mai kamar wuya a ce shi kan shi Ferfesa Doyin ya yi wani abu na a zo a gani a wannan takaitaccen lokaci.”

Shi ma Abdulmunafi Usman cewa ya yi. “shi shugaba Muhammadu Buhari har yau duk da gashi wata goma sha bakwai ya rage mishi ya sauka, bai yi wannan tunanin ba a ganin cewa kila kafin ya bar mulki ya bar wani abu, ko ya farfado da wani abu da ya ruguje a baya. Aka ci gaba da haka za’a iya cewa to abunda mu ka zata gare shi bai samu ba Kenan.”

Masanin tattalin arzikin kasa Dakta Yusha’u Aliyu ya ba da shawara ga gwamnati shugaba da ma sabon mai ba shi shawara kan tattalin arzikin kasa.

“Farko zai duba kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi korafi akai, sannan kuma idan wannan kasafin kudin aka ci gaba da sa’insa akai tsakanin shugaba Buhari da ‘yan majalisa a cikin abubuwan da kasafin kudin ya kunsa to wannan zai fi haifar da tarnaki ne ga tafiyar tattalin arzikin kasa.”

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tattalin Arziki – Masana - 3'46"