KALLABI: Hira Da Linda Umaru PT1 Da Nazari Kan Kalubalen Rayuwa A Najeriya

Alheri Grace Abdu

Shirin kallabi na wannan makon, wanda ya kasance na farko a shekara ta 2024, ya yi nazarin kalubale da aka fuskanta a Najeriya a shekarar da ta gabata tare da bada shawarwari kan yadda za a sami ingancin rayuwa a bana. Bakin da muka gayyata domin tsokaci kan wannan mukala sun hada da malamar makaranta Khadija Idris, da matar wani mai Unguwa, Jamila Hamisu Mai Iyali, da kuma uwargida uwar daki, Abida Sani.

Kallabin shirin ta mako kuma ita ce, Linda Umaru, wata 'yar asalin jihar Gombe da take da bude katamfaren shago da take sanarkitso da saida kayan kitso, tana kuma sayar da abincin gida Najeriya, da ta yi fice ainun a jihar California.

Your browser doesn’t support HTML5

Kallabi-Linda Umaru PT1