Tsohon ministan tsaron Najeriyan ne dai Janar TY Danjuma,mai murabus shine ya soma takalo maganar, a jawabinda yayi a taron yaye daliban jami’ar jihar Taraba,inda ya bukaci ‘yan kasar da su tashi tsaye su kare kansu domin a cewarsa jami’an sojin kasar ba zasu kare su ba daga wadanda ya kira yan ina da kisa.
Tsohon ministan ,wanda shima tsohon soja ne,ya kuma zargi sojin kasar da daurewa yan ta’adda gindi a tashe tashen hankulan dake faruwa a kasar.
‘’Dole mu tashi tsaye,dole mu ki,dole kowa ne dan kasa ya tashi tsaye don kare kansa,tunda dai sojoji suna daurewa yan ta’adda gindi,suna kashe jama’a ,kai sojojin ne ma ke basu hanyar tafiya.
‘’ To muddin kun dogara ga sojoji su kare ku,to labudda dukkan mu zamu mutu! Don haka dole kowa ya kare kansa,’’ a cewar tsohon ministan tsaron Najeriyan Janar TY Danjuma.
To sai dai kuma da alamun kalaman tsohon ministan,ya soma jawo cece-kuce a kasar. Buba Yero Mafindi wani tsohon dan kishin kasa ne,da kuma Muhammad Lawal Danladi malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa,sun bayyana ra’ayin su.
Yayin da wasu ke suka,shi kuwa wani tsohon jami’in tsaro Mallam Danladi Mayo Ranewo, yana ganin akwai bukatar karatun ta natsu ga kalaman da manyan Najeriya ke yi ayanzu.
Kawo yanzu tuni rundunan sojin kasar ta fitar da martani game da zargin da tsohon ministan keyi, inda daraktan yada labaran rundunan sojin Birgediya Janar Texas Chukwu a sanarwar da ya fitar, yace basu nuna sonkai ko wariya game da abubuwan dake faruwa ko suka faru a jihohin Binuwai da Taraba. Haka nan kuma rundunan tace abun takaici ne kalaman Janar TY Danujman,musamman a wannan lokaci da ake nemo bakin zaren magance tashe tashen hankulan dake faruwa a kasar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5