WASHINGTON, DC —
An kaiwa jerin gwanon motocin kakakin majalisar dattawan Najeriya hari tsakanin kudu maso gabashin kasar da kudu maso kudun kasar lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa jana'iza.
Alhaji Abdulmajid Ali kwamishanan 'yansandan jihar Imo da aka tambayeshi sai yace su ma haka suka ji cewa an kaiwa tawagar motocinsa hari. Yace sun fara binciken inda abun ya faru. Hatta shi kakakin majalisar dattawan Sanata David Mark bai fadi inda aka kai masa harin ba yayin da yake jawabi a cocin da ya je sujadar jana'izar da ta kaishi. Sai dai yace tun daga ta wajen jihar Imo ya shigo kila a jihar aka kai masa hari.
Amma an ce lamarin ya faru ne wajejen Orlu kuma jami'an dake tare da shi sun yi musayar wuta da wadanda suka kai ma tawagarsa hari. Kwamishanan 'yansandan yace akwai 'yan fashi ta wajejen hanyar da ta fito daga Enugu. Tana yiwuwa 'yan fashin dake wurin ne suka kai masa hari.
Kawo yanzu dai babu kowa da aka kama inji Alhaji Ali kwamishanan rundunar 'yansandan Imo. Saidai mataimakin babban sifeton 'yansanda dake jihar Imo ya soma kaddamar da binciken lamarin.
Ga rahoton Lamido Abubakar

Your browser doesn’t support HTML5