Mukaddashin alkalin alkalan Ambrose Mamadi ya rantsar da kakakin majalisar Ahmed Sintiri a cikin wani tsauraran matakan tsaro a matsayin mukaddashin gwamnan jihar.
Ahmed Sintiri zai cigaba da zama mukaddashin gwamnan jihar har na watanni uku kafin a yi sabon zabe. Karo na biyu ke nan da Ahmed Sintiri zai zama mukaddashin gwamnan jihar.
Yayin da yake mai da kalamu akan sake rike wannan mukamin yace ya godewa Allah. Yace yana taya mutanen Adamawa murna domin yakin da majalisar ta yi na jihar ne. Yace zasu yi gwamnatin bisa adalci tsakaninsu da Allah. Zasu kuma tabbatar kowa ya samu hakinsa. Yace basu da wata jiha sai Adamawa. Dole su dawo karkashin jihar su ginata domin ta cigaba. Ya kira manyan mutanen Adamawa su hada kai a gina jihar.
Daga Abuja uwar jam'iyyar PDP ta tura tawaga zuwa rantsar da mukaddashin gwamnan a karkashin Alhaji Mustapha Buhari ma'ajin jam'iyyar na kasa. Yace sun zo ne su ga abun da ya faru kuma suna yiwa Allah godiya. Yanzu jama'ar Adamawa sun samu canjin da suke nema.
To har yanzu jam'iyyar APC wadda aka tsige gwamnanta bata ce komi ba tukunna.
Masu nazari kamar Alhaji Musa Jika na kungiyar kare hakin dan Adam yace akwai abun dubawa. Inji shi abun da ya faru a jihar Adamawa wani abun kunya ne ga arewa baki daya. Majalisar Adamawa bata yiwa kanta adalci ba. Bata yiwa jama'ar Adamawa adalci ba. Bata yiwa dimokradiya adalci ba. A ganinsa 'yan majalisar sun tafka kuskure babba kuma nan gaba zasu yi da na sani. Lamarin zai dingi zaga jihohin ne domin yanzu ana cewa saura jihar Nasarawa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5