Kakakin Boko Haram Ya Ce Ba Su Ne Ke Kai Hare-Hare Ba

Tankin yakin Boko Haram.

Wanda aka ce shi ne kakakin kungiyar ne ya furta hakan a tattaunawar su da Umar Farouk Musa.

Wakilan kungiyar Boko Haram da na gwamnatin kasar Najeriya na ci gaba da tattaunawa a N’Djamena babban birnin kasar Chadi a karkashin jagorancin shugaban kasar Idriss Deby.

A daidai wannan lokaci ne wanda aka ce shi ne kakakin kungiyar ta Boko Haram Danladi Ahmadu yake cewa ba fa ‘yan kungiyar na asali ba ne ke ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan arewacin Najeriya, kuma ya kara da cewa su na goyon bayan duk matakin da sojojin Najeriya ke dauka na neman tarwatsa masu kai hare-haren, sannan y ace Allah Ya toni asirin su.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba 'yan Boko Haram ne ke kai hare-hare ba,inji wanda ake cewa shi ne kakakin su.- 2':02"

Wakilin Sashen Hausa a Abuja Umar Farouk Musa ne ya tattauna da Danladi Ahmadun wanda aka ce shi ne kakakin kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya ke zaman neman sasantawa da ita a kasar Chadi.