Masu gangamin sun ta'allaka karuwar kashe kashe a yankin Akan kalaman da gwamnan jihar ta Kaduna yayi na batun daukar fansa kafin zabe, abin da suka ce ya kara rura wutar rikicin.
Jagoran matasan Adara na kasa Laminus Paul yace duk rikice rikicin da ake yi a kudancin Kaduna ba inda abin yafi tsananta kamar kasar Adara. Abin da yake cewa Babban abin bakin ciki ne sosai.
Alheri Bawa Magaji Wacce ta yi korafin gwamnatin Kaduna ta Kama Masu dattawansu na Adara ciki har da mahaifinta bayan wani rikici, tayi korafin yadda har yanzu ake ci gaba da tsare dattawan, batare da gaba tar dasu gaban kotu ba.
Baki dayan masu zanga zangar sun ce sun zo Abuja don gayawa duniya halin da suke ciki inda kullum ake ta kashe su kuma ba wani mataki da aka dauka akai.
Amma cikin martanin da ya mayar, kakakin gwamnatin jihar Kaduna Samuel Aruwam ya ce ba gaskiya bane duk zarge zargen da sukewa gwamnatin, Yana mai cewa ba yadda za a yi gwamna yayi kalaman da zasu tunzura Jama'a.
Dangane kuma da batun kakkame dattawan Adara, mai magana da yawun gwamnan yace wannan ba aikin gwamna bane ba jami'an tsaro , kuma bai ba daidai bane a sa gwamna cikin batun.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5