Kafar sada zumunta ta whatsApp bata daukar duk matakan da suka kamata wajen kare bayanan mutane daga gwamnatoci, a cewar kungiyar masu da’awar kare bayanan mutane na sirri.
Kungiyar Electronic Frontier Foundation wadda ke ikirarin kare muradun al’umma a yanar gizo, ta baiwa kafar WhatsApp maki mafi ‘kankanta a rahotanta na shekara-shekara kan yadda kafafen sada zumunta ke kare bayanan masu amfani da shafukan.
Wannan sako na zuwa ne duk da cewa WhatsApp ta kirkiri hanyar kare bayanan masu amfani da kafar wadda ake kira end to end encryption da kuma hawa kujerar naki da ta yi wajen hana gwamnatoci sakonnin da wasu masu laifi suka aika ta kafar.
WhatsApp da shafin Amazon baki ‘dayansu sun sami tauraro biyu cikin biyar, wadda hakan ke zama mafi karancin maki.
Wasu bayanan kotu na nuni da cewa gwamnatoci sun umarci kamfanin ya mika bayanan mutane domin taimakawa wajen bincike-bincike.
Kungiyoyin sun fara kalubalantar WhatsApp tun shekarar da ta gabata, lokacin da kamfanin ya fara musayar bayanan mutane zuwa shafin Facebook.
Your browser doesn’t support HTML5