Kafafen Yada Labarai Sun Shiga Yajin Aiki a Jamhuriyar Nijar

Shugabannin gidajen Talibijan da Radiyo masu zaman kansu na kasar Nijar

Kafafen yada labarai masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar, sun shiga yajin aikin kwana guda bayan da gwamnati ta fara wani shirin binciken kudaden haraji da suka biya a baya.

A Jamhuriyar Nijar, kafafen yada labarai masu zaman kansu sun shiga yajin aiki na wuni guda a yau Litinin.

Yajin aikin wani mataki ne da kafafen yada labaran suka dauka da nufin nuna rashin jin dadinsu akan wani shirin bincike da gwamnatin kasar ke shirin kaddamarwa.

A ranar Larabar, hukumomin kasar shirin fara tantance wadanda suka biya haraji daga shekarar 2013 ya zuwa yanzu.

A kungiyar hadaklar kafafen yada labarai ta Nijar, wannan yunkuri ne na rufe bakin ‘yan jarida masu zaman kansu.

“A ka’ida wannan ba matsala ba ce, wanda ya saba biya a kowace shekara akwai takardu akwai komai, sannan bayan haka sai a zo a ce maka za a zo a duba shekara hudu ko biyar, za a zo a sake dubawa a ga ko ka biya ko baka biya ba, muna tsammanin akwai zan ce a kasa.” Inji Abdurrahman Mustapha Zangoma, mamba a kungiyar kafafen yada labaran.

Babban Magatakarda a ofishin Ministan sadarwa a Jamhuriyar ta Nijar, Aboulaye Coulibaly, ya ce yana cikin wani taro, a lokacin da wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma ya nemi jin ta bakin gwamnati.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu kan wannan lamari:

Your browser doesn’t support HTML5

Kafafen Yada Labarai Sun Shiga Yajin Aiki a Jamhuriyar Nijar - 3'15"