Wasu 'yan arewa dake zaune a Legas sun bayyana rashin yarda mai karfi ga shawarar da wasu, ciki har da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ke bayarwa na kafa rundunar 'yan sanda a jihohin kasar.
Daya daga cikin irin wadannan mutane, Alhaji Garba Abdullahi Wazirin hausawan Jihar Legas, yace kafa 'yan sandan jihohi tamkar raba Najeriya ne. Yayi misali da yadda jami'an hukumomin Jihar Legas, wadanda ba wani makami suke rike da shi ba, suke tursasawa mutanen da ba 'yan kabilarsu ba ne, balle kuma an samu 'yan sanda da makamai.
Alhaji Abubakar Chiroman Hausawan Jihar Legas, shi kuma cewa yayi idan har manyan arewa zasu yarda a ba jihohi iznin kafa rundunonin 'yan sanda, to ya kamata kuma a ba kowace jiha iznin kafa rundunar sojanta, domin tabbatar da rabuwar kasar kamar yadda masu hankoron haka ke nufi.
Yace maimakon a zauna ana wani boye-boye, gara kawai a ce an raba kasa kowa ya kama gabansa ya koma inda ya fito. Yace su 'yan arewa dake zaune a kudu, sune kadai suka san irin ukubar da suke sha.
Sai dai kuma wani wanda bai fadi sunansa ba, yace an jima ana ta ce za a yi, amma ba a yi ba, don haka shi a ganinsa, gara ma kawai a yi din a samu zaman lafiya.
Sai dai kuma wakilinmu Babangida Jibrin, yace ba a san ko shugaba Muhammadu Buhari zai amince ad wannan matakin na kafa rundunonin 'yan sandan jihohi kamar yadda mataimakinsa da kuma wasu gwamnoni ke neman da a yi ba.
Your browser doesn’t support HTML5