Karamar hukumar Ikara dai na cikin kananan hukumomin da Allah ya tarfawa garin su nono game da matsalar tsaro, saboda ba a taba samun rahoton harin 'yan-bindiga a karamar hukumar ba. Sai dai mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ASP Mansur Hassan ya ce ana zargin akwai wanda 'yan bindigan su ka biyo.
ASP Mansur ya ce rahotanni sun tabbar da cewa tun da yamma wasu suka ga wadannan 'yan bindigar akan babura su na sayen abinci amma ba wanda ya sanar da jami'an tsaro kafin aikata aika-aikar da su ka yi da daddare.
Malam Musa Saya-Saya na cikin 'yan uwan malam Adamu mai wankin hulan da ke cikin wadanda maharan su ka kashe kuma ya ce kaddara ce kawai ta rutsa da dan uwan na su.
Daya daga cikin masu aikin tsaron al'uma a karamar hukumar Ikara wanda ke cikin na farko-farkon da suka isa masallacin ya ce basu taba ganin irin wannan kisa ba.
Ya ce lokacin da su ka isa sun iske gawarwaki da kuma jini a kan shimfidar masallaci kuma mutane na cikin damuwa saboda ba su saba ganin irin wannan musiba ba.
Karamar hukumar Ikara dai na makwabtaka da kananan hukumomin Makarfi, Soba, Kubau da kuma Tudun Wandan Kano kuma dukkanin wadannan kananan hukumomi ba sa samun matsalar hare haren 'yan-bindiga kamar yadda lamarin ya addabi kananan hukumomin Kaduna ta tsakiya.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5