Shugaban rundunar sojan kasa na sojojin kasa da kasa a yakin da ake gudanarwa a Iraqi, ya shawarci sojojin nasu da cewa kada suji ujila ko zafin nama a kokarin da suke na kama garin Mosul, ta yadda har hanzarin nasu cikin gaggawa zai budewa abokan adawarsu hanyoyin ci musu zarafi.
WASHINGTON, DC —
A hirarsa da yan jarida ta wayar tarho a jiya Laraba a birnin Bagadaza, Maj-General Gary Volesky yace bai kamata sojojin Iraqin su yi hanzarin shiga Mosul ba, akwai bukatar tukuna su fara samun karfi da matsawa abokan adawarsu lamba.
Amurka tana bada tallafin mayaka, kayan aiki, da jiragenta na sama dake kai dubban hare hare, har ma da jirage masu saukar ungulu a matsayin gudunmuwa a yakin yanto birnin na Mosul.
Amma duk da haka ba wannan ne kadai kwamandan sojan hadin guiwan ya mayar da hankali akai ba. Gen. Volesky yace da gangan aka warwatsa wasu sojojin Amurka zuwa wasu yankuna na daban a cikin kasar ta Iraq don hanawa mayakan IS damar kaura wasu yankuna dda fatar juya hankalin gwamnatin Iraqi zuwa kudancin kasar.