Kace-Nace A Jihar Taraba Ya Hana A Rabawa Yan Gudun Hijira Kayan Tallafi

Sanata Aisha Jummai Alhassan Ministar Harkokin Mata Da Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz

Yayin da yan gudun hijira a jihar Taraba ke ci gaba da kokawa kan rashin samun kayayyakin tallafi da gwamnatin tarayya ta turo jihar, biyo bayan takaddamar data kaure a tsakanin gwamnan jihar da kuma Ministan harkokin mata.

Yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda jam’iyar APC ke zargin ana neman karkatar da kayakin, zargin da gwamnatin jihar ke musantawa.

Shugabanin jam’iyar APC a sun kira wani taron manema labarai a jihar, inda suka bayyana abin da ya faru a tsakanin gwamnatin jihar da kuma wakiliyar shugaban kasa kuma Ministan harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan da abun takaici kasancewa yan gudun hijira ne wannan fadan ta shafa.

Wannan cacar baka dai na zuwa ne yayin da yan gudun hijira a jihar ke kokawa na halin kunci da suke ciki, batun da yasa shugabanin jam’iyar APC a jihar Taraba kiran wani taron manema labarai inda suka koka tare da zargin cewa da wata manufa gwamnan jihar ya hana a raba kayakin tallafi da gwamnatin tarayya da turo jihar, inda ta yi zargin cewa gwamnantin na neman karkatar da kayakin ne, zargin da ko mukarraban gwamnan jihar ke musantawa.

Shugaban jam’iyar APC a jihar Taraban, Alhaji Hassan Jika Ardo, ya bayyana abun da ya faru a tsakanin gwamnatin jihar da kuma wakiliyar shugaban kasa kuma Ministan harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan da abun takaici kasancewa yan gudun hijira ne fadan ta shafa.

To sai dai kuma, a martanin da gwamnan jihar Taraban ya maida, ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin siyasa Alhaji Abubakar Bawa, yace ai ba laifinsu bane, Ministar ceta tsokano su.

Koda yake a martanin da ita kuma ta maida, Ministan ta musanta zargin cewa akwai wata kullalliya a tsakaninta da gwamnan jihar Akitet Darius Dickson Isiyaku.

Koma da menene dai fatan dai yan gudun hijiran shine a samu sasantawa ko a samu a raba musu kayakin.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kace-Nace A Jihar Taraba Ya Hana A Rabawa Yan Gudun Hijira Kayan Tallafi - 3'43"