Su dai wadannan al’umman Bwate na kabilar Bachama da suka fito daga kauyukan Lawaru,Dong , da Bayan a karamar hukumar Demsa da kuma na kauyukan Nzoruwe,Pulum,Shaforon da Kodomti dake cikin karamar hukumar Numan sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya data kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin hukumta wadanda ke da hannu a harin bom da suke zargin rundunan sojin samar kasar sun kai musu inda mutum 78 suka mutu a kwanaki.
Lamarin dai ya faru ne yayin da rundunar sojin saman ta je raba yayin rikici a tsakanin makiyaya da manoma a wadannan yankuna.
Da yake jawabi a taron manema labarai da suka kira, a Yola, shugaban kungiyar Farfesa Wunosiko Nzita ya ce suna bukatar rundunar sojin ta fito ta amsa laifin da aka aikata,da kuma bada hakuri amma ba musanta abun da ya faru ba.
Haka nan ya ce,su tuni suka shirya don gurfanar da dakarun sojin saman dama gwamnatin Najeriya,gaban kotun duniya ta ICC.
Su kuwa Mr Bosin Yakana, da Tony Mabulti sun bayyana hanyoyin da za’a bi domin a samu zaman lafiya musamman a tsakanin makiyaya da manoma a wadannan yankuna.
Tun farko ma dai sai da kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoton ta inda ta soki rundunar sojin saman,yayin da ita kuma a bangarenta rundunar sojin saman ta fitar da nata martani a Abuja,inda ta musanta zargin. Wannan ma kuma na zuwa ne yayinda hankula ke soma kwantawa a wadannan wurare dake kudancin jihar Adamawan.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5