A watan Maris ne dai Najeriya ta gudanar da zabukanta a matakai daban-daban ciki har da na gwamnoni da na shugaban kasa cikin nasara, kuma wasu da dama na ganin watsi da aka yi da nuna banbancin addini da kablianci ya sa aka samu nasara.
Wakilin Muryar Amurka Hassan Ummaru Tambuwal da ke birnin Ibadan a jahar Oyo ya zanta da wasu kabilu dake zaune a birnin kan me suke ganin ya janyo nasarar yin zaben cikin kwanciyar hankali.
“Kamar a ce wannan yayana ne wannan ba nawa ba ne, wannan musulmi ne wannan kirista ne, hakan bai ya tasiri a wannan zabe ba.” Inji Peter Eze, shugaban al’umar Igbo a karamar hukumar Akinyele.
Shi ma sarkin al’umar Hausawa a Akinyelen, Alhaji Yaro Abubakar, ya ce sam al’adar nuna banbanci tsakanin ‘yan Najeriya ba ta yi tasiri ba.
Wannan “al’ada ba ta yi tasiri ba saboda a da irin siyasar da ake yi ta uban-gida kamar a yammacin kasar nan da muke yanzu duk ta kau, hakan ya sa an ture wannan dabi’ar ta wannan wane ne wancan wane ne” Inji Alhaji Abubakar.
Najeriya kasa ce da ta yi fama da nuna banbance banbance na kabilanci da na addinin a harkokin siyasarta, wanda hakan ya tsunduma kasar cikin rudani da dama.
Ga karin bayani a rahoton da Hassan Ummaru Tambuwal ya hada mana:
Your browser doesn’t support HTML5