Mai girma alkalin babban kotun kolin Najeriya ya zama ubangida kuma bango majinginin abun tinkahon jama'a, mai daidaito da tabbatar da adalci da gaskiya, inji Mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Osinbajo.
Farfasa Yemi Osinbajo wanda yayi magana cikin sassauyar murya da ban tausayi yaci gaba da cewa zama alkalin alkalan kasa wani babban nauyi ne da ya maida dan Adama tamkar Ubangij Allah Madaukakin Sarki. Ya gayawa alkalin cewa yana da iko kan rayuwa na mutane baki daya. Kana da ikon tabbatar da mulkin mai mulki ko kuma ka fitar dashi daga mulki.Kana da ikon sa ido akan duk alkalai, inji Farfasa Osinbajo.
Bayan an rantsar dashi sabon alkalin alkalan Walter Onnoghen yace ya tabbatarwa al'ummar kasar zaman lafiya ta hanyar aikata gaskiya da adalci a harkokin shari'a.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5