JTF ta Kama Jiragen Satar Mai Fiye da 255 a Niger Delta

Mayakan kungiyar MEND

Kakakin rundunar JTF a yankin Niger-Delta, Leftana-Kanar Anka Mustapha, yace sun kuma lalata dubban durom-durom na mai tare da sako wasu mutanen da aka sace.

Rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF a yankin Niger-Delta ta bayyana cewar ta samu nasarori da yawa a yunkurinta na wanzar da tsaro a wannan yankin a yayin da Najeriya take shirin gudanar da babban zabe a wata mai zuwa.

Kakakin rundunar, Leftana-Kanar Anka Mustapha, ya fadawa VOA Hausa cewa sun kama manyan jiragen ruwan satar man fetur guda 55, da wasu kananan jiragen ruwan guda 200.

Haka kuma sun samu nasarar kamawa da lalata wuraren tace danyen man fetur na haramun da kuma dubban durom-durom da ake amfani da su wajen jigilarsu.

A wani gefen kuma, Kanar Mustapha yace sun samu nasarar kwatow asu sanannun mutanen da barayi suka sace su, su na yin garkuwa da su domin neman diyya.

Ya bayyana cewa rundunar sojan Najeriya ta yi alkawarin kara musu kananan jiragen ruwan kwale-kwale na sintiri da suke da su domin tabbatar da cewa sun samu nasarar ayyukansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Kama Jiragen Satar Man Fetur Fiye Da 255 A Niger-Delta In Ji JTF - 3'05"