Tsohon kocin kungiyoyin PC Porto da Sporting Lisbon, zai rattaba hannu ne kan kwantaragin shekara 1 da Najeriya, wanda za’a iya tsawaitawa bisa la’akari da kwazon aikinsa.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta NFF ta amince kan gajeruwar kwantaragi ne sakamako takaddamar shari’ar biyan kudade da yanzu suke ciki da tsohon kocin kasar Gernot Rohr, wanda hukumar kwallon duniya wato FIFA, ta umarci NFF din ta biya shi kudi dalar Amurka d.380, saboda saba ka’idodin kwantaragi.
Peseiro mai shekaru 62 da haihuwa, ya yi murabus daga horar da ‘yan wasan kasar Venezuela a watan Agustan da ya gabata, sakamakon matsalar rashin biyan sa albashi da hakkokinsa.
A can baya kadan a watan Fabrairu, sai da Najeriyar ta ba da sanarwar daukar shi aikin horar da ‘yan wasan kasar, amma kuma daga baya lamarin ya wargaje saboda kasa cimma daidaito a tsakaninsu.
A yanzu kuma Peseiro zai soma aiki na Najeriya ne nan take, tare da wasanni 2 na sada zumunta da kasar za ta buga da kasashen Ecuador da Mexico a kasar Amurka, kafin daga bisani a shiga buga wasannin neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2023.
A Ingila kuma, sabon mai horar da ‘yan wasan Manchester United da zai soma aiki, Erik Ten Hag, ya bayyana yadda kungiyar ta kasa samun gurbin fafata gasar zakarun Turai a kakar wasanni mai zuwa da cewa lamari ne maras dadi.
Ten Hag ya ajiye aikinsa na horar da ‘yan wasan kungiyar Ayax tun kafin kwantaraginsa ya kare, domin komawa United.
Yanzu haka United din na matsayin ta 6 a teburin gasar Premier tare da maki 58, yayin da ya rage mata wasa daya ta gasar ta bana, da za ta fafata da Crystal Palace.
Wannan ne sakamako mafi muni da kungiyar ta samu a gasar ta Premier a tarihi, kasancewar ta sami nasara ne a wasanni 16 kacal daga cikin wasanni 37 da ta buga, lamarin da bai yi wa ten Hag dadi ba.
A daya bangaren kuma mai horar da ‘yan wasan kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya saki karin yiwuwar lashe gasar Premier ta bana, duk kuwa da cewa jagororin gasar wato Manchester City, sun barar da maki, a yayin da suka yi kunnen doki da West Ham a jiya Lahadi.
Kunnen dokin dai na nufin bambancin maki 4 tsakanin City din da Liverpool wadda ke da bashin wasa daya kafin wasar karshe ta gasar, yayin da kuma za’a iya tantance zakara ne kadai a ranar karshe ta gasar ta Premier.
Ko ma dai me ya faru, Manchester city na bukatar yin galaba kan Aston Villa domin lashe gasar ta bana.
Shahararren dan wasan Uruguay Luis Suarez ya yi ban kwana da kungiyarsa ta taka leda Atletico Madrid, a yayin da yake kan hanyarsa ta barin kungiyar a wannan bazara.
Suarez mai shekaru 35, ya koma Atletico din ne daga Barcelona, shekaru 2 da suka gabata, bayan da mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta Barcelona ya nemi ya wuce.
Atletico din ta ba da sanarwar tafiyar dan wasan kafin soma wasan da ta buga da Sevilla a jiya Lahadi, inda kuma Suarez ya sami kyakkyawar karramawa da jinjina daga masoyan kungiyar, musamman a karshen wasan.
Duk da yake dai ba’a kai ga bayyana kungiyar da Suarez zai koma ba, wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar komawar sa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona.
Saurari rahoton Murtala Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5