Alkalumma sun rawaito cewa wannan batu dai ya tunzura tsohon shugaban rundunar sojojin Najeriya Janar T.Y Danjuma mai ritaya, har ya fito fili karara, ya kalubalanci fadar shugaban kasa da ta kama wadannan mutane ta hukunta su.
Wannan furuci da T.Y Danjuma yayi, shine karo na farko da wani babba zai fito daga yankin Arewa, yana tsawatawa a game da ire-iren wadannan munanan kalamai.
Mainasara Koba Ibrahim, masani ne a harkar tsaro, siyasa da huldar kasashen duniya, ya yaba da wannan yunkuri da T.Y Danjuma yayi.
“Na farko dai, abune na a gode mashi, kuma ko a gida idan aka kasance babu manya, to al-amura su kan kasance sun tabarbare”, a cewar Mr. Ibrahim.
Kashi na farko a tsarin mulki yace Najeriya kasa ce dunkulalla, mai al-ummomi daban-daban, tare da kabiloli da addinai daban-daban, inda kundun ya baiwa kowa hakkin a dama da shi, kuma a kare masa mutuncin kansa.
Mai magana da yawun ofishin kyamfe na Janar Muhammadu Buhari, Naja’atu Muhammed ke cewa anyi wa kundun tsarin mulki karan tsaye.
“Na farko dai, wannan cin amanan kasa ne. In kaci amanar Najeriya, kundun tsarin mulki cewa yayi a kama ka, a kashe ka.”
Sai dai kuma, Isa Tafida Mafindi, mai magana da yawun ofishin Shugaba Goodluck Jonathan yace mutan arewa basu da wani da zasu yi alfahari da shi kamar Goodluck Jonathan.
“Ai in akwai gwanin da ya wuce Jonathan, to mutanen ‘social media’ suke sarrafa wannan. Mu kuma, muna nunawa a kasa cewa Jonathan dinnan, a sake zabensa”, a cewar Mafindi.
Yanzu haka dai, kungiyoyi masu zaman kansu na mata da matasa na yin gangami da kuma yekuwa a kafafen yada labarai wajen gargadin ‘yan siyasa game da hadarin dake akwai a siyasar ko-a-mutu, ko-a-yi-rai.
Your browser doesn’t support HTML5