John Bolton Ya ce A Shirye Yake Ya Bada Sheda A Majalisar Dattijai

Tsohon mai baiwa Sshugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro John Bolton.

Tsohon mai baiwa shugaban Amurka shawara akan sha’anin tsaro John Bolton, a jiya Litinin ya ce zai bayyana domin ba da shaida a zaman sauraren karar tsige shugaba Donald Trump idan har majalisar dattawa ta gayyace shi.

A baya, shugaba Donald Trump ya umurci jami'an sa kada su amsa gayyatar majalia. Amsa gayyatar majalisar da Bolton yace zai yi, zai baiwa Democrats Karin haske kan ainihin abin da ya faru a bayan fage akan yunkurin Trump na tursasawa Ukrain gudanar da bincike da zai amfane shi a siyasance.

Bolton, wani mai akidar jaddada karfin ikon fada a ji da Amurka take da shi a duniya, yayi aiki a matsayin jami’in tsaro na 3 na Trump tsawon watanni 17 kafin a cire shi a watan Satumban da ya gabata, sakamakon takaddama akan yadda za’a tafiyar da dangantaka da Iran, Korea ta Arewa da Afghanistan.

A shirye-shiryen kada kuri’ar tsige Trump a majalisar wakilai, masu bincike sun ki gayyatar Bolton, saboda fargabar tsawaita zaman shari’a a kotu, akan ko za’a iya tilasta masa ba da shaida, ko kuma zai yi biyayya ga umarnin Trump da ya hana wa manyan jami’ai bayar da shaida.

A yayin da zaman sauraren karar ta tsige Trump ya koma a majalisar dattawa, duk da yake ba’a tsayar da ranar somawa ba, Bolton ya ce zai so ya warware wasu al’amura masu sarkakiya gwargwadon iyawar sa, cikin kyakkyawar natsuwa da kuma nazari.