JOHESU Ta Ayyana Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 7

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya na Najeriya (JOHESU) ta ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7, tun daga tsakad daren yau Juma’a.

Yajin aikin baya-bayan nan na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da kungiyar ta baiwa gwamnatin Najeriya.

Yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja, shugaban JOHESU na kasa, Kabiru Minjibir, ya zayyana wasu daga cikin bukatun nasu.

Bukatun sun hada da gaggauta aiwatar da dunkulallen tsarin albashin ma’aikatan jinya da biyan karin kaso 25 cikin 100 na basussukan da suke bin gwamnatin daga watan Yuni zuwa Disambar 2023 da kara shekarun ritayar ma’aikatan jinya da kuma yafe haraji a kan kudaden alawus din ma’aikatan jinya da kuma gaggauta biyan bashin alawus din shiga hatsari na lokacin annobar korona.

Kungiyar ta bukaci dukkanin mambobinta dake fadin Najeriya su yi biyayya ga wannan umarni.