Joe Biden Ya Bayyana Takaicin Sa Game Da Kalaman Trump

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana takaicinsa game da kalaman da shugaba Donald Trump ya fada a ranar Litinin, cewa zai yi amfani da karfin soji wajen dakile tarzomar da ta barke a kasar, sanadiyar mutuwar wani bakar fata a makon da ya gabata. Mutumin ya mutu ne a hannun 'yan sanda yayin da su ke kokarin kama shi a Minneapolis.

A wani bayani da aka nuna ta talabijin a fadar White House, shugaban ya fadi cewa, "idan jihohi su ka kasa daukan matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin jama’a, to zan aike da sojojin Amurka su dau mataki".

Wannan furuci na shi na yin amfani da sashe 1870 na dokokin kasar da ya bawa shugaba damar ya dau matakin kare al’umma a yanayi na gaggawa.

A baya bayan nan anyi amfani da wannan doka ne a shekara 1992, a yayin wata tarzoma a Los Angeles, biyo bayan duka da ‘yan sanda suka yi wa Rodney King wani dan Amurka bakar fata.