JNI Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Yunkurin Tilastawa Wasu Matasa Su Sauya Addininsu

 JNI Jos, jihar Filato

Sakataren majami’ar ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu ya shaida wa Muryar Amurka cewa ECWA, da ma sauran kungiyoyin addinin Kirista ba sa tilasta mutum shiga addinin, ba tare da amincewarsa ba.

PLATEAU, NAJERIYA -Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen Jihar Filato ta kalubalanci hukumomi da su gudanar da bincike kan wasu yara Musulmai da Cocin ECWA ta tsare su da niyyar sauya musu addini.

Bayanai na nuni da cewa, a ranar goma sha hudu ga wannan wata na Yunin 2022 ne hukumar tsaron farar kaya ta DSS, ta kai samane a wani gida dake yankin Tudun Wada a birnin Jos, inda ta fito da yaran da aka kebe su ake koyaddasu karatun addinin kirista da sana’o’i.

Daraktan agaji na kungiyar Jama’atu Nasril Islam a Jihar Filato, Danjuma Khalid ya ce sun sami labarin ne bayan daya daga cikin yaran mai suna Abdulrahaman Usaini da aka dauko shi daga Jihar Gombe ya tsallaka ganuwar gidan ya tsere, daga bisani aka kai shi ofishin Jama’atu Nasril Islam a garin Jos inda jami’an kungiyar suka kai maganar ofishin hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Ku Duba Wannan Ma Nuna Banbancin Kabila Ko Addini Ke Maida Hannun Agogo Baya A Najeriya: Kungiyar Fulani Kiristoci

Abdulrahman Usaini wanda ya ce shi ‘dan asalin garin Azare ne a Jihar Bauchi ya kubuta ne tare da wani Nura Usama.

Abdulrahman Usaini ya yi bayani kan irin rayuwar da suke yi a cikin gidan da aka killace su, wanda ya ce ana koya musu karatu na Baibul, da batun aure da zaman gida da sauransu.

Sakataren majami’ar ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu kuwa ya shaida wa Muryar Amurka cewa ECWA, da ma sauran kungiyoyin addinin Kirista ba su tilasta mutum shiga addinin, ba tare da amincewar sa ba.

Rabaran Nmadu ya kara da cewa hukumar tsaron farar kaya tana nan tana gudanar da bincike kan lamarin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar JNI Ta Kalubalanci Hukumomi A Jos Su Bincika Zargin Canza Wa Wasu Yara Addini.mp3