Jiya shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya karbi karin bayani akan kasafin kudin da majalisar kasa ta bashi bayan da ta yi wasu 'yan kwaskwarima tare da rage kudin da yake son ya kashe.
Da farko an samu kace-nace dangane da bayanan da aka kai masa inda yace shi ba zai rabtaba hannu a kasafin ba sai ya samu cikakken bayanan da ya kamata ya sani. Musamman yana son ya san dalilan da ya sa majalisar ta rage wasu kudade da kuma tabbatar cewa kasafin kudin da ya mika majalisar ta duba.
Malam Garba Shehu kakakin shugaban ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan lamarin.Yace yau Juma'a da safe majalisar ministoci zata zauna ta duba kasafin kudin dalla dalla da zummar tabbar cewa kasafin da suka mika aka yi aiki a kai.
Tantancewar ta zama wajibi saboda yadda wasu suka sauya kasafin da shugaban kasa ya gabatarwa majalisa da wani daban. Saboda haka ,inistocin zasu duba su ga ko abun da aka dawo masu dashi daidai yake da abun da suka bayar baicin wasu gyare-gyare. Idan akwai banbancin da har zai gurgunta kasafin to sai a sake mayarwa majalisa ta yi abun da ya kamata.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5