Duk da yake anyi masa kisan gilla, amma ya bar muna kyawawan halayensa na tsare adalci da tabbatar da zaman lafiya, inji Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke magana a jiya laraba, gameda kwarzon yakin kare 'yancin Bil'Adama Rev. Martin Luther King, a zagayowar ranar da aka yi masa kissan gilla shekaru 50 da suka wuce, a'lamarin d a ya auku a birnin Memphis a jhar Tennessee.
Kashe King da akayi a shekarar 1968 wanda ya biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban Amurka John F Kennedy a shekarar 1963, da kuma shima gwarzon yakin kare hakkin Bil'Adama Malcox X a shekarar 1965, wadannan sun haifar da zanga-zanga a wasu manyan biranen Amurka, ciki ko harda nan Washington D C, da Baltimore, da New York da Detroit, da Chicago da birnin Kansas.
A jiya laraba a nan Washington D C, masu zanga zanga sun shiga jerin wadanda suka yi maci cikin lumana daga hasumiyar tunawa da shi king har zuwa babban dandalin taro na kasa anan fadar Amurkan.
A birnin Memphis ma anyi gangami domin tunawa da Dr. king tare da masu jawabai, ciki ko harda dan takarar shugaban kasa a jamiyyar Democrat bannie Sanders,wakilai da kungiyar bakar fata 'yan majalisar dokokin ta tarayya,shugabannin addinai, dana kwadago.