Dubban mutane sun yi maci a tsawon Gandun Wuraren Tarihi na National Mall, har zuwa Ginin Majalisar Dokokin Amurka ta Capitol, a nan birnin Washington DC jiya Lahadi, su na kiran da a kara samar da agaji ga yankin Puerto Rico da mahaukaciyar guguwa ta daidaita.
Watanni biyu bayan da mahaukaciyar guguwar Maria ta yi kaca-kaca da wannan tsibiri, kimanin rabin jama’arsa, har yanzu ba su da wutar lantarki sannan wasunsu ba su da tsabtataccen ruwa.
“A Puerto Rico mu na da maza da mata masu fama. Akwai bukatar mu taimaki ‘yan’uwanmu Amurkawa. Ya kamata mu sake maido da martabar Puerto Rico,” a cewar daya daga cikin masu zanga-zangar.
Da dama daga cikin masu zanga-zangar ta jiya Lahadi sun yi kiran da Fadar Shugaban Amurka ta White House ta soke ‘Dokar Jones’ wata dokar da aka kirkiro a 1920, wadda ta ce jirgin ruwa mai dauke da tutar Amurka ne kadai, banda jirgin ruwan wata kasa, zai iya dakon kaya daga wata gabar Amurka zuwa wata.
An shafe aikin dokar game da batun kai kayan tallafi zuwa Puerto Rico. To amma masu suka na cewa da ba don dokar ba, da an samar da kayan agajin tun ma kafin lokacin da aka jingine ta.