A Tanzania 'yan kasar sun jefa kuri'ar don su zabi sabon shugaban kasa da 'yan majalisa, a zabenda ake ganin da wuya ace ga wanda zai kai labari kai tsaye a kasar dake gabashin Afirka.
Wakiliyar Muryar Amurka Jill Craig ta ziyarci runfunan zabe masu yawa a Dar es Salam a jiya Lahadi. Tace an gudanar da zaben cikin lumana ba tareda cikas ba, bab kuma tarzoma.
Jam'iyyar CCM wacce ta juma tana mulkin kasar tana fuskantar matsin lamba sai ta gaggauta yin ayyukan da zasu kawo ci gaba ga kasar cikin hanzari, kuma ta tunkari matsanancin talauci da al'uma suke fama da shi, duk da haka masu fashin baki sun ce zata sami nasara. Jam'iyyar ta fuskanci hamayya daga gamayyar jam'iyyun masu adawa wadanda suka tsaida tsohon Firayim Ministan kasar Edward Lowassa.
Shugaban kasar na yanzu Jakaya Kikwete ba zai sake takara ba saboda ya gama wa'adi biyu da tsarin mulkin kasar ya kayyade.
A Ivory Coast ma 'yan kasar sun jefa kuri'a a zaben shugaban kasa jiya Lahadin. Shugaban kasa mai ci Alassane Ouattara, wanda ake gani babu tantama zai samu nasara yace yana son "samun gagarumar rinjaye a zagayen farko".
Ana kallon zaben na jiya a zaman zakaran gwajin dafi a zaben kasar, bayan tarzomar da ta biyo bayan zaben da aka yi kasar shekaru biyar da suka wuce har aka halaka mutane akalla dubu uku.
'Yan takara shida ne suke kalubale ga shugaban kasar dan shekaru 73 da haifuwa.
A kasar Haiti 'yan kasar sun je rumfunan zabe domin su zabi sabon shugaban kasa, akasar da tafi ko wacce talauci a nahiyar Amurka. Zaben ka iya zama mataki da zai baiwa kasar damar kawar da mummunan rikicin siyasa da teke ciki.
Rahotani suka ce mutane sun fito kwai da kwarkwata, a zaben da fiyeda mutane 50 suke takarar shugabancin kasar.
A turai, jam'iyyar PIS a Poland ta ayyana kanta a zaman wacce ta sami nasara a zaben wakilan majalisa da aka gudanar jiya Lahadi, bayan watanni tana kamfen cewa zata kara kashe kudade domin kyautata jin dadin jama'a, da nuna adawa kan amfani da takardun kudin Euro, da kuma kekashe kasa na nuna adawa da samarda mafaka ga musulmi wadnada suke gudun hijira a cikin kasar.