Amurka ta dakatar da bayar da duk wata visa ta zuwa kasar daga Turkiyya, wadda ba ta masu kaura ba, har zuwa wani lokaci, a cewar ofishin jakadancin Amurkar da ke birnin Ankara.
Wata takardar bayanin ofishin jakadancin wadda ta fito jiya Lahadi na cewa, "Wasu al'amura na baya-bayan nan sun tilasta Amurka sake nazari kan yadda gwamnatin Turkiyya ke daukar tsaron lafiyar ofishin jakadancin Amurka da kuma ma'aikatansa"
Takardar ba ta yi cikakken bayanin dalilin sake nazarin ba, da kuma ko wannan dakatarwar ta tsawon wani lokaci ce.
'Yan sa'o'i bayan nan sai Turkiyya ta mai da martani da sanarwar cewa ita ma ta dakatar da bayar da tata visa ga Amurkawa dake son zuwa kasarta, ta na mai amfani da irin lafazin da Amurka ta yi amfani da shi wajen dakatar da tata visar.