Manyan mutanen da suka halarci gagarumin taron laccar karshe na kyamfen din nata da aka yi jiya a birnin Philadelphia da ya samu halartar dubban mutane, sun hada da shugaban Amurka na yanzu Barack Obama da matarsa Michelle, da mijinta kuma tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da ‘yarsu Chelsea , hade da manyan mawaka irinsu Bruce Springsteen da Jon Bon Jovi.
A jawabinsa a wurin, shugaba Obama ya neme Amurkawa da su fito yau Talata su zabi Hilary Clinton, wacce yace duk shugabannin duniya suna kallonta da idon mutunci da kima.
Bayan birnin Philadelphia, gangamin zasu wuce ne zuwa jihar Carolina ta Arewa inda za’a ci gaba da irin wannan gagarumin taron laccar inda kuma daga cikin wadanda ake sa ran zasu bayyana a wurin harda shahararriyar mawakiyar nan mai suna Lady Gaga.
Shi kuma Donald Trump, dan takaran jam’iyyar Republican, shima jiya ya halarci manyan tarukkan lacca a jihohi da dama da dole sai ya lashe su in yana son zama shugaban Amurka – kamar Florida, Michigan, New Hampshire da Pennsylvania.
Dukkan ra’ayoyin jama’a da ake dauka dai na nuna cewa Hilary Clinton na kan gaban Trump wajen farin jinin jama’a, kuma itace ake ganin alamar kamar zata lashe zaben.