Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitacen Tahirin Hillary Clinton 'Yar Takarar Shugabar Kasa Ta Jam'iyyar Democrat


Hillary Clinton dake takarar zama shugabar Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton dake takarar zama shugabar Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat

Shekaru 8 da suka gabata saura kiris Hillary Clinton taci zaben tsayar da dan takarn shugaban kasa na jam’iyyar Democrat amma kash, bata samu ba, duk da cewa ta samu kuri’u 18m.

Sabon jini Sanata Barack Obama shi ya samu galaba a kanta.

Amma a wannan karon, hakarta ta cimma ruwa don kuwa a yau itace ‘yar takarar jam’iyyarta ta shugaban kasa a zaben wannan shekara, kuma tana kyautata zato zata haye tudun natsira (wanda ke hanawa mata kaiwa wannan matsayin),ta zama shugabar kasa.

Idan har taci zaben wannan watan na Nuwamba zata yi abin tarihin zama maccen da ta tashi daga zama matar shugaban kasa zuwa zama Sanatar jihar New York zuwa zama sakatariyar harkokin wajen Amurka, yau ga shi ta karkare a matsayin shugabar Amurka baki dayanta.

Ra’ayoyin Amurkawa sun nuna ana sonta amma kuma har wayau ana kyamarta.

Hillary Clinton na cikin mutanen da suka fi suna a duniya.

Wadanda suka yi kusa da ita sun ce mace ce mai rungumar mutane da kuma son yin ba’a. Amma duk da haka ba ta kan so ta bayyana kanta a baina jama’a ba.

Saboda haka wasu suna yi mata kallon marasa gaskiya.

An sha bincikenta har an gaji. Binciken baya bayan nan an yi ne akan yadda tayi anfani da na’urarta ta aika sakkonin email din kanta yayinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka a gwamnatin Obama, mukamin da ta rike har na tsawon shekaru hudu.

Ita dai Hillary an haifeta ne a gida mai matsakaicin arziki kusa da Chicago a shekarar 1947.

Cikin wani littafin tarihin rayuwarta da aka wallafa a shekarar 2003 Hillary Rodham Clinton ta fada cewa tayi kuruciya cikin dadi da walwala.

Mahaifinta wani rikakken dan jam’iyyar Republican ne amma taceta shiga siyasa ta kuma zama ‘yar jam’iyyar Democrat sanadiyar mahaifiyarta, wacce itama ‘yar jam’iyyar Democrats din ce.

Sai dai kuma lokacin da take matashiya, Hilary ta chanja sheka, ta koma‘yar jam’iyyar Republican

Hilary dai tayi karatu a kwalajin mata ta Wellesley, a nan ne kuma kara tsunduma cikin siyasa har ma ta bada jawabin sauke karatu a makarantar tasu a shekarar 1969.

Daga baya ne Hillary Clinton tayi karatun zama lauya a Jami’ar Yale inda ta sake sauya sheka daga jam’iyyar Republican zuwa Democrat. A wannan makarantar ce kuma ta hadu da mutumin da karshenta zai zama mijinta, Bill Clinton a dakin karatu. Ita da Bill Clinton sun yi aure a shekarar 1975.

Bayan da suka yi aure ta bishi zuwa jiharsa ta asali Arkansas inda aka zabeshi ya zama gwamna a shekarar 1978.

Diyarsu daya tilo, Chelsea, an haifeta ne a Arkansas.

A shekarar 1992 aka zabi Bill Clinton shugaban kasar Amurka har ma yanzu yana ba’a yana cewaya ba kasar shugabannin biyu da farashin daya – ma’ana shi da matar tashi.

A matsayinta na matar shugaban kasa, Hilary ta cigaba da yin siyasa amma ta kasa samun nasarar samar ma jama’a insura ta kiwon lafiya.

A zamansu a fadar White House rade-radin yin lalata da mata da Bill Clinton yake yi sun cika fadar har zuwa lokacinda aka kamashi da wata matashiya mai suna Monica Lewinsky, abinda yassa har Majalisar wakilai ta tsigeshi amma ta dattawa ta wanke shi.

Bayan da suka bar fadar White House Hillary Clinton ta cigaba tana fafutikar tsayawa da kanta a faggen siyasa.

Ta dalilin haka ne mutanen New York suka zabeta Sanata (‘yar Majalisar Dattawa) a shekarar 2000, kuma suka sake zabarta a shekarar 2006 a karo na biyu.

A shekarar 2008 Shugaba Obama ya nada Hilary Clinton a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Kawo yanzu Hillary Clinton ta ziyarci kasashen duniya 112 inda take ta jaddada batun ‘yancin mata da tasirin aiyukkan diflomasiya wajen inganta cudanyar kasashe.

Shugaba Obama da matarsa Michelle suna goyon bayan Hillary Clinton dari bisa dari. Yayinda tayi jawabi a babban taron tsaida ‘yan takara na jam’iyyar su ta Democrat, Michelle Obama ta yabawa Hillary Clinton bisa ayyuka da tayi da kuma halayenta, inda Michelle din ke cewa, “babban abinda ke bani sha’awa da Hillary Clinton shine cewa bata bada kai bori ya hau saboda matsi. Ba zata taba bin wata hanya ba domin saukinta. Haka kuma Hillary Clinton bata taba yin kasa a gwuiwa ba domin ranta”, inji Michelle.

Yanzu kam Hillary Clinton na bukatar duk wani jajircewa saboda ta samu kanta a fafatikar siyasa mafi tsanani a rayuwarta, inda take fuskantar wani fitacce, sannanen Ba’amurke Dan Duniya kuma hamshakin attajiri Donald Trump.

Shima, kamar Clinton an sanshi a duk fadin duniya amma mai raba kawunan jama’a ne.

Ra’ayin masu kada kuri’a na nuna cewa ‘yan takaran biyu suna kunnne doki a tagomashinsu wajen masu jefa kuri’a. To saidai kuma tarihin Hillary Clinton yana nuna cewa zata cigaba da yaki har karshe, sai ta ga abun da ya tubewa Buzu nadi ranar zabe 8 ga wannan watan Nuwamba – wacce itace ranar zaben sabon shugaban kasa a Amurka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG