Jiya Aka Rantsar da Diaz Canal a Matsayin Sabon Shugaban Cuba

Sabon shugaban Cuba Miguel Diaz-Canal.

Bayan ya yi mulki na shekaru 10 Raul Castro ya mikawa Miguel Diaz-Canal dan shekara 57 mulkin kasar a matsayin sabon shugaban kasa wanda bashi da alaka da iyalan Castro

An bayyana Miguel Diaz-Canal a matsayin sabon shugaban kasar Cuba , wanda wannan shine karo na farko a cikin shekaru 60 akasar mai mulkin tsarin kwaminisanci zata samu shugaban da alaka da iyalan Castro.

Wannan dan talikin dan shekaru 57, Diaz Canal shine kadai dan takara daya tilo wanda yayi nasarar samun aikin shugabancin kasar na wa’adin shekaru 5 kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ke cewa.

Sai dai wannan sabon sauyin shugaban kasa da kasar ta samu ba a sa ran ya kawo wani canji mai tasiri ba, domin jim kadan da rantsad dashi a jiya alhamis Diaz-Canal yayi alkawarin ci gaba da tafiyar da mulkin kasar kan tafarkin tsarin na kwaminisanci irin na Castro.

‘’Wannan damar da ‘yan kasa suka bayar, suna fata ne suga an ci gaba daga inda aka tsaya a mulkin juyin juya hali mai tarihi, inji Diaz-Canal.

Shi dai sabon shugaban shine mataimakin shugaban kasa, ga bisa dukkan alamu yana da ra’ayin sasauci abinda ya sa ya zamo karbabbe ga dattawan da suka samar wa kasar ‘yanci sakamakon juyin juya hali ke nan.

Diaz Canal ya gaji Raul Castro ne dan shekaru 86 wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 10.

Raul dai shima ya gaji yayansa ne Fidel Castro wanda ya shugabanci kasar a matsayin Prime Minista daga baya kuma ya koma shugban kasa bayan wani juyin juya hali da aka yi a kasar a shekarar 1959, kuma Fidel Castro ya sauka daga karagar mulki ne a shekarar 2006 lokacin da ya fara rashin lafiya.