Amma wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan kwanaki da bayanai ke nunin cewa jirgin mai daukar jiragen yaki da wasu jiragen ruwa sun kama hanyarsu zuwa yankin.
Ranar 11 ga wannan watan da muke ciki ne shugaba Donald Trump ya ce zamu aika da Armada, wato babban jirgin yakin Amurka, kwanaki uku kenan bayan da jirgin ya bar kasar Singapore.
Kwamandan sojin Amurka a yankin Pacific, Admiral Harry Harris, ya fada aranar tara ga watan Afrilu cewar ya umarci rukunin mayakan ruwan da su nufi arewa bayan sun bar Singapore kuma wannan na nuna ba za a ci gaba da tsarin farko na zuwa gabar Australia ba.
A jiya Laraba dai, jami’an Amurka sun yi ta kokarin fayyace labarai masu cin karo da juna a kan inda rukunin mayakan ruwan suke.
Kakakin fadar White House Sean Spicer, ya tabbatar da maganar shugaba Trump cewar sun tura jiragen yaki. Yace wannan itace gaskiyar Magana kuma hakan ne ke faruwa.